News
Alhazai Miliyan Biyu Ke Shirin Hawan Arafah Ranar Talata
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Alhazan duniya kimanin milIyan biyu ciki har da ‘yan Najeriya ne ke shirin hawan Arafah a ranar Talata, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke da burin yi wa kasar addu’ar zaman lafiya.
Kimanin Musulmi miliyan biyu daga kasashen duniya dari da sittin ke shirin hawan Arafah a shekarar 2023. Ranar Arfa dai ita ce mafi muhimmanci a aikin Hajji.
Hankali Ya Koma Kan Nada Sabbin ‘Yan Majalisar Zartarwa Da Tinubu Zai Nada
Wannan karon shi ne aikin Hajji da ya fi samun jama’a tun bayan dawowa daga hutun dole a sakamakon barkewar annobar cutar Coronavirus da ta addabi duniya.
Jaridar Gazzete da ake bugawa a kasar Saudiyya, ta ambaci ministan kula da aikin Hajji da Umara na kasar Dr. Taufiq Al’rabiah ya na cewa a aikin Hajji na shekara ta 2023, an janye duk wasu ka’idodi da suka shafi cutar Coronavirus.
Tuni dai suma sauran Alhazan Najeriya da suka halarci aikin Hajjin suka ce sun shirya tsayuwar Arfa ta ranar Talata.
Muhammad Awwal Aliyu, sakataren hukumar Alhazan jihar Neja a Najeriya, ya fadi cewa sun shirya motoci domin daukar Alhazan Najeriya da kuma fita da wuri saboda rage cunkoso.
Batun addu’ar neman zaman lafiya da arzikin kasa na daga cikin abin da Alhazan na Najeriya ke da niyyar roka a filin Arfa, musamman manoma a wannan lokacin na damina.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
