Connect with us

News

Shehu Sani Ya Bukaci Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci Da Sauransu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministocinsa da tsoffin shugabannin tsaro na gwamnatinsa.

Sani ya ce ya kamata shugaban kasa Tinubu ya binciki laifukan tattalin arziki da aka tafka a karkashin gwamnatin Buhari cike da karfin gwiwa.

Gwamnatin Jihar Kano Zata Saka Gina Ginin Da Ta Rushe Na Shataletalen Gidan Gwamna

Ya ce sauya fasalin naira ba shi kadai ne laifin tattalin arziki da aka aikata ba sannan kama mutum daya ko biyu ba zai samar da amsar da ake bukata ba.

Advertisement

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @ShehuSani, ya ce ya kamata shugaban kasa Tinubu ya fara bincike daga kan Buhari har zuwa kan na kewaye da gwamnatinsa.

Yace “Sauya fasalin naira ba shi kadai ne laifin tattalin arziki da aka tafka ba a karkashin gwamnatin Buhari.”

“Ya kamata shugaban kasar ya yi karfin halin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru a gwamnatin Buhar, ta hanyar farawa da Buhari, tsoffin ministocinsa, shugabannin tsaronsa da na kewaye da gwamnatinsa.”

“Haka kuma bai kamata shugaban kasar ya tsame tsoffin gwamnoni wadanda suka samu yanci yanzu, harma suke jiran samun mukaman siyasa daga wannan bincike ba.

“Kange mutum daya ko biyu ba zai bayar da amsa ga laifukan da sauran suka tafka ba a shekaru takwas da suka wuce.”

“Cikin sauki za a dauki binciken da ke gudana a yanzu a matsayin na son kai idan aka takaita binciken.”

Advertisement

“Tambaya mai sauki ita ce; ya batun sauran mutane da suka bayar da gudunmawa wajen lalata tattalin arzikin? Ko kuma dai wasunmu suna da gajen hakuri ne saboda rashin masaniya kan abun da ke tunkaru mu.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending