News
Babu sulhu tsakaninmu da ‘yan bindiga – Gwamnatin Zamfara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce ba za ta yi sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar, a wani sabon mataki na samar da tsaro a jihar
Hakan na zuwa ne a yayin da ‘yan bindigar ke ci gaba da kashe mutane tare da satar wasu domin karbar kudin fansa.
Arc. Ahmad Abba Yusuf yana taya al’ummar Kano murnar bikin Sallah.
Sabanin tsarin tsohuwar gwamnatin jihar Zamfara na tataunawa da ‘yan bindiga da zummar kawo ƙarshen zubar da jini, a yanzu gwam
natin Zamfara ta PDP ta nuna cewar babu batun sulhu tsakaninta da ‘yan bindiga.
Babban mataimakin gwamnan jahar Zamfara akan kafafen watsa labarai Malam Mustapha Muhammad Kaura, ya ce sabuwar gwamnatinsu ba za ta lamunci yin sulhu da ɗan bindiga ko ɗan ta’adda ba.
Ya ci gaba da cewa ”Shi tsari na sulhu ba zai yiyu a ce gwamnati ce ke neman sulhu, in ma ta ce tana neman sulhu to yaudara ce, domin kuwa sulhun nan yau shekara 13 ana wannan maganaa jihar zamfara”.
”Shin ka zo ka yi sulhu da ‘yan bindiga a kan me? a kan ka kasa? Sai an karbe makamai”, Malam Mustapha Muhammad Kaura
Ya ce babu wani matakin da gwamnatin za ta ɗauka da ya wuce murkushe ‘yan bindigar.
A shekarun baya dai, tsohon gwamnan jahar Zamfara, Bello Mutawalle, ya yi ta bukukuwan yin sulhu da ‘yan bindiga.
To sai dai bisa ga dukkan alamu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
