News
Masu zanga-zanga sun kona gidan wani magajin gari a Paris
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A ranar Lahadi, Fira minister Faransa, Élisabeth Borne ta yi tir da harin da masu zaga-zanga suka kai gidan wani magajin gari na wani birni a kewaye birnin Paris, inda har suka banka wa gidan wuta, harin da ta bayyana a matsayin abin takaici.
Borne ta yi kira da a hukunta wadanda suka aikata wannan aika aika a gidan magajin garin L’Hay-Les Roses, Vincent Jeanburn.
Rikicin Kabilanci Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Biyu A Jihar Taraba
Jeanburn ya ce mai dakinsa da ‘yayansa biyu, masu shekaru 7 da 5 sun samu rauni a yayin da suke tserewa daga wannan farmaki da masu zanga zanga suka kai musu.
Da take ziyarar birnin na L’Haÿ-les-Roses a ranar Lahadi, Fira ministar ta ce ba zai yiwu a kyale wadanda suka aikata wannan mummunan aiki ba.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
