Connect with us

News

Rikicin Kabilanci Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Biyu A Jihar Taraba

Published

on

Police

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Gwamnatin jihar Taraba ta ayyana dokar ta baci a karamar hukumar Karim Lamido sakamakon wani rikicin kabilanci da ya yi sanadin kashe akalla mutane biyu da kuma yin kone-kone a kauyuka fiye da bakwai da suka haddasa asarar dukiyoyi.

Advertisement

Muryar amurka ta rawaito cewa Alhaji Tanko Babbo Abbo Andami, daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya na yankin Karim Lamido kuma daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, ya ce a cikin dare da misalin karfe biyu suka samu labarin harin har an kashe wani yaro, dayan kuma sai da aka kai shi asibiti ya cika.

Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya sake jaddada alkawarin shawo kan kalubalen tsaron Najeriya

Rikicin ya kuma haddasa kone-kone a kauyukan da lamarin ya whafa wanda hakan yasa da yawa daga cikin mazauna kauyukan yin Kaura zuwa cikin garin Jalingo babban birnin jihar.

Advertisement

Rundunanr ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da faruwar rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutanen biyu da kuma kone-kone, kamar yadda kakakin rudunar SP Usman Abdullahi ya bayyana.

Alhaji Ahmed Umar Karim, dan asalin garin Karimjo ne kuma daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, ya ce rikicin ya samo asali ne sakamakon nadin Sarkin Wurkun da gwamnatin jihar da ta wuce ta yi bayan mutuwar tsohon Sarkin.

Advertisement

Hon. Muhammad Audu, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ardo Kwala Lau da Karim Lamido a Majalisar Wakilan tarayyar Najeriya, ya yi kira ga dukkan bangarorin biyu da su yi hakuri su kai zuciya nesa domin a samu a kawowa yankin ci gaba mai dorewa da zaman lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending