News
Gwamnatin Jihar Anambra Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Zargin ‘Daliba Da Karawa Kanta Makin Jarabawar UTME A bana
Gwamnatin Jihar Anambra ta kafa wani kwamitin bincike kan cece-kucen da ya biyo bayan zargin kara maki da ake yiwa wadda tafi kowa hazaka a jarrabawar UTME ta shekarar 2023.
A baya an sanar da cewa Ejikeme ‘yar shekara 16 daliba a makarantar sakandaren ‘yan mata ta Anglican da ke Nnewi ta samu maki 362 a matsayin wacce ta fi kowacce kokari.
Gwamnatin tarayya za ta soma aiki da na’ura don karbar haraji daga ‘yan tireda
Sai dai a wata sanarwa da hukumar JAMB ta fitar, ta yi watsi da sakamakon nata a matsayin na bogi, inda ta ce an yi magudi kuma za a gurfanar da ita a gaban kuliya.
Sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Anambra ta fitar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a Mr Nnaemeka Egwuonwu, ta bayyana cewa binciken zai bankado gaskiyar yadda Ejikeme ta samu sakamakon nata.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
