Connect with us

News

Kungiyoyin Yaki Da Rashawa Sun Bukaci A Sanya Idanu Akan Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wata kungiyar farar hula, mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bukaci rundunar ‘yan sandan kasa da kasa  da sauran hukumomin da abin ya shafa da su sanya tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano cikin jerin sunayen wadanda ake sa Ido akansu kan badakalar bidiyon dala.

Jagoran kungiyar, Comrade Kabiru Saidu Dakata ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Kano, inda ya ce Ganduje zai iya ficewa daga kasarnan ba da dadewa ba.

Advertisement

Ko Shugaban Kasa Tinubu Ya Bani Mukami Bazan Karba Ba – Fayose

Dakata ya zargi Ganduje da yin amfani da umarnin kotu a matsayin dabarun jinkiri wajen yin zagon kasa ga binciken faifan bidiyo na Dala, yayinda abokansa na siyasa ke takama da cewa Ganduje nada goyon bayan fadar shugaban kasa.

Ya ce kamata ya yi gwamnatin da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta ta kare martabarta ta hanyar kammala binciken Ganduje domin kaucewa kafa hujjar cewa Najeriya nada kantar cin hanci da rashawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending