Connect with us

News

An Kori Wani  Dan Majalisa Yayin Zama Saboda Yin Shigar Da Ba Ta Dace Ba

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Idanu sun koma kan wani dan Majalisar Wakilan Najeriya a ranar Laraba lokacin da aka bukaci ya fice daga zauren majalisar saboda yin shigar da ba ta dace ba.

Dan majalisar, wanda ba a iya tantance sunansa ba, saboda yana cikin sabbin wadanda da aka rantsar a watan jiya, ya shiga zauren ne da wata rigar T-shet mai launin ja, da kuma wani tsukakken wando.

Advertisement

Bikin Rantsar da Sabbin Kwamishinonin jihar Jigawa.

Bayan shigowarsa, dan majalisar, wanda kuma ya zo a makare, ya nemi wajen zama a zauren majalisar, ana dab da karkare zama.

Sai dai jim kadan bayan ya zauna, sai dan majalisa Billy Osaweru, ya jawo hankalin Kakakin majalisar cewa wanda ya shigo ya yi shigar da ba ta dace ba.

Advertisement

A cewar Billy, shigar dan majalisar ta saba da tsarin saka suttura cikin mutunci na majalisar.

Hakan ne ya sa Kakakin ya bukacin dan majalisar ya fice daga zauren, inda kuma ya yi hakan ba tare da bata lokaci ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending