News
Za a bai wa iyalai miliyan 12 naira 8,000 na tsawon wata shida
Advertisements

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin kasar na bai wa gidajen talakawan Najeriya miliyan 12 Naira 8,000 na tsawon watanni shida.
Hakan na kunshe cikin wata wasika da shugaban kasar ya rubuta wa majalisar wakilai dangane da bukatar gwamnatin Buhari ta karbo bashin dala miliyan 800 domin shirin samar da tsaro na zaman lafiya.
Shugaban kasar na neman amincewar majalisar ne domin samun bashin.
Don tabbatar da gaskiya, Shugaban ya ce za a tura kudin zuwa asusun aiyarsu ta bank.
Advertisements
