News
Rundunar ‘Yan sanda sun kama masu tilasta zama a gida su 26 a Imo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta kama wasu mutane 26 da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta (IPOB).
Rundunar ‘yan sandan jihar ta kuma gurfanar da wasu mutane 53 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da hada baki akan, fashi da makami, kisan kai, lalata, garkuwa da mutane, fataucin yara, mallakar haramtattun makamai ba bisa ka’ida ba, kwace mota da lalata wutar lantarki.
Za a bai wa iyalai miliyan 12 naira 8,000 na tsawon wata shida
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye ya shaidawa manema labarai cewa an kama jami’an tsaro na zaman gida ne bayan sun yi harbi da ‘yan sanda a unguwar Irete da ke kan titin Onitsha inda suke aiwatar da dokar zama a gida ba bisa ka’ida ba.
A ci gaba da gudanar da bincike kan laifukan da sauran mutane 53 da ake zargin suka aikata, jimillar bindigu guda 32 da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai 70, motoci biyar da aka kwace amma aka kwato, an kwato babura bakwai.
