News
Karancin Masara Na Neman Durkusar Da Kiwon Kaji A Kasar nan.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar masu kiwon kaji a Najeriya ta ce wuraren kiwon kaji na rufewa saboda cigaba da fuskantar tsadar farashin masara.
Masara babban bangare ne, wanda ya ƙunshi kashi 60 zuwa kashi 70 cikin ɗari na abincin kaji.
Gwamnatin jahar Kano Na Binciken Zargin Badakalar Sama Da Billiyan 100 A Mulkin Ganduje.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Sunday Ezeobiora, ya fitar, ta ce masana’antar kiwon kaji a Najeriya na gab da rushewa gaba daya idan gwamnati ba ta yi gaggawar shiga cikin al’amarin ba.
Rahotanni sunce, saboda matsalar, farashin ƙwai, wanda shine tushen sinadarin furotin ga ƴan Najeriya da dama, ya yi tashin gwauron zabi da sama da kashi 118.34 cikin ɗari bayan da aka samu koma bayan na yawan shigo da masara da kashi 97.91 cikin ɗari.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
