Connect with us

News

Sojojin sama sun yi luguden wuta kan manyan yan bindigar da suka addabi jihar Katsina da Zamfara

Published

on

Yan bindiga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Rundunar sojin sama ta bayyana nasarar hallaka manyan yan bindigar da suka addabi yankin Arewa maso yammacin Nijeriya musamman yankin Zamfara da Katsina

Kamar yadda Katsina Daily News ta rawaito daga jaridar Daily News ta ta wallafa labarin tun da sanyin safiyar yau Laraba, majiyar ta Daily Trust din ta bayyana cewa wani rahoton da ta samu daga rundunar sojin ya bayyana cewa sojojin sama dake a Rundunar Hadarin Daji ne suka yi nasarar hallaka manyan yan bindigar a harin da suka kai ranar 28, da 29 July 2023.

Advertisement

Tinubu ya nada Atiku Bagudu, Bello Matawalle, Simon Lalong da karin mutum 16 ministoci

Majiyar ta rawaito cewa a wani harin da Sojojin suka kai a yankin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, sun yi nasarar kashe manyan yan bindiga 16, ciki har da wanda ya fi shahara sosai da aka fi sani da Dankarami.

Haka kuma sun kashe Adamu Aleru a wani harin da suka kai kan yan bindigar da aka ba su labarin sun sato mutane da shanu a yankin Tsafe ta jihar Zamfara da kuma Faskari ta jihar Katsina.

Advertisement

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin sama Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce Shugaban rundunar sojin sama Staff, Air Marshal Hassan Abubakar ya kara jami’ansa a yankin domin fatattakar yan bindiga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending