News
Sojojin Jumhuriyar Nijar sun naɗa sabon Firaminista
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Jagoran sojojin jumhuriyar da suka yi juyin mulki a Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da tsohon ministan kuɗin ƙasar a matsayin sabon firaminista.
Ali Mahaman Lamine Zeine ya maye gurbin Mahamadou Ouhoumoudou wanda yake Turai lokacin da aka yi juyin mulkin.
kungiyar kwadago ta NLC Ta Janye Shirinta Na Fara Yajin Aiki
Mista Zeine, ya rike muƙamin ministan kuɗi daga shekara ta 2001 zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatin tsohon shugaba Mamadou Tandja a 2010.
Ya taɓa yin aiki a bankin bunƙasa Afrika, a ƙasashen Chadi da Ivory Coast da kuma Gabon, kuma shi ne ya mallakin kamfanin yaɗa labarai na ActuNiger.
Advertisements
