News
Hanyar shiga Maƙabartar Kuka bulukiya ta Zama Barazana ga mazauna Unguwannin Dala.

DAGA ISAH MAGAJI RIJIYA BIYU
Al’umma mazauna Unguwannin Dala sun koka kan yadda Hanyar shiga Maƙabartar Kuka bulukiyata lalace da kuma Ruftawar Kabarurruka a Maƙabartar.
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa mazauna Unguwannin sun koka sakamakon mamakon Ruwan sama da aka fara yi hakan ya sanya hanyar bata biyuwa gaba-daya ko Mutawa aka yi to sai dai ayi dogon Sha tale tale Sannan za’a kai mamaci makwancinsa.
Sun kara da cewar suna fuskantar Barazanar Rashin Tsaro a wannan hanya ta shiga Maƙabartar Bulukiya inda akewa hanyar laƙabi da Ruwan Hassan da Usaini,ta yadda wurin ke zama mafakar ɓata gari da kuma masu shaye_shaye.
A baya bayan nan Ɗan majalisa mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala a zauren Majalisar Jihar Kano Hon Lawan Hussaini ya sha alwashin yin duk mai yi wuwa ganin an cike wannan Ramin to sai dai kuma Haryanzu shiru sema ƙara lalacewa da gurin yayi.
Na samu Tattaunawa da mai unguwar Dala Malam Ɗaha Yusuf ya shaida cewar suna iya kokarin su akan wannan hanya kuma suma karfinsu ya kare don haka suna kira da gwamnati data taimaka tai aikin gurin acikin kankanin lokaci,ya kara da cewar a rika turo da babbar mota wadda zata rika bude hanyar .
