News
Jami’an KAROTA Sunyi Arangama Da Matuka Baburan Adaidaita Sahu A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA sun yi arangama da masu tuka babur din Adaidaita sahu a Kano Kusa da Gadar kofar Nasarawa .
Rikicin dai ya sa matasa suka yi zaman dirshan na tsawon mintuna, yayin da gungun jama’a suka rika kai wa mutane hari ba tare da kakkautawa ba.
Shedun gani da ido sun bayyana cewa, tawagar jami’an KAROTA ne suka kakkabo wani direban babun Adaidaita sahu da ya yi kuskure, amma ya ki tsayawa.
Wani shaidan gani da ido wanda kawai ya bayyana sunansa da Sani ya ce, “Jami’an KAROTA ne suka bukaci wani matshi da ya tsaya amma sai ya ci gaba da tafiya. Jami’an KAROTA sun ja babur din Adaidaita sahu ta fadi. Ya lalace kuma wani fasinja ya ji rauni a kafadarsa. Ina tsammanin ya sami karaya.”
Jim kadan bayan haka ne masu babur din Adaidaita sahu suka afkawa ofishin KAROTA dake daura da wurin da lamarin ya faru wanda ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin biyu.
“masu babur din Adaidaita sahu sun ci gaba da sauke fasinjoji a wurin don tallafa wa membansu. Sai da zuwan ‘yan sanda suka shawo kan lamarin,” in ji Sani.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya shugabancin hukumar a kokarin da yake yi na sauya hukumar tare da kawo sauye-sauye .
Da aka tuntubi Kakakin KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Naisa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sanar da ‘yan sanda kuma suna gudanar da bincike kan lamarin.
Ki
