Connect with us

News

Dakta Labaran ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawuran da ya dauka na kiwon lafiya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Advertisement

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawuran da ya dauka kan harkar kiwon lafiya a jihar Kano.

Kwamishinan ya yi wannan yabon ne a wata tattaunawa da ya yi da wani kamfanin sadarwa, da sashin hulda da jama’a na ma’aikatar ya bibiya.

Advertisement

Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 31 a Adamawa

Ya ce sake fasalin tsarin kiwon lafiya na jihar na daya daga cikin manyan manufofin Engr. Abba Kabir Yusuf, shi ya sa bai yi kasa a gwiwa ba, da ya hau kan mulki ya dauki tsattsauran matakai don gyara abubuwan da suka sabawa doka da oda.

Dr. Labaran ya yi nuni da cewa gwamnan mai kishin harkar lafiya ya cika wasu alkawuran, yayin da wasu kuma ke gab da cikawa.

Advertisement

Ya ce, “Mai girma Gwamna ya yi alkawarin bayar da tallafin haihuwa kyauta ga matan jihar, wanda ya cika wannan alkawari saboda a kwanakin baya na raba magunguna da sauran kayayyakin kuka da kafiyar mata masu juna biyu na Naira miliyan 53 ga cibiyoyin lafiya daban-daban domin amfanin mata masu juna biyu da wadanda za su haihu ta hanyar taimako na musamman.

Dakta Labaran ya kuma bayyana cewa, a lokacin yakin neman zabensa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin dawo da asibitin kananan yara na Hasiya Bayero wanda shi ne asibitin kananan yara a jihar wanda ke da gadaje 86, wanda majinya majinyata 3,000 zuwa 5,000 ke ziyarta a kullum.

Advertisement

Ya kara da cewa abin takaici, gwamnatin da ta shude ta sayar da asibitin ga wasu ‘yan baranda a kan kudi Naira miliyan shida, alhalin farashinsa ya haura Naira biliyan 6. Ya ci gaba cewa, mai girma gwamna a lokacin yakin neman zabensa, ya sha alwashin karbar asibitin daga hannun duk wanda aka siyar da shi tare da mayar da shi ga jama’ar jihar Kano.

“Gwamnan ya ziyarci asibitin cikin sa’o’i 48 da rantsar da shi kuma ya zaga ko’ina. Nan da nan ya umurci ma’aikatar lafiya da takwararta ta ayyuka da su fara aiki a wannan asibitin”, a cewar kwamishinan
Game da shirin kula da lafiya har cikin al’umma kuwa, Dakta Labaran ya bayyana cewa, mai girma gwamna ya umarci ma’aikatarsa da ta shiga wurare masu wuyar ziyarta da al’umomin yankuna ke shan wahala wajen zuwa cibiyoyin lafiya domin a duba su tare da ba su magani kyauta na kananan cututtukan da suke fama da su, sannan a tura su manyan asibitoci game da manyan cututtuka.
Kwamishinan ya yi nuni da cewa, lokacin da gwamnati mai ci ta zo ta gano cewa adadin likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya ba su isa ba, cikin farin ciki ya ce an umurci ma’aikatarsa da ta tantance irin bukatar da jihar ke da ita dangane da ma’aikatan lafiya tare da isar da su ga gwamnati inda girma gwamna zai yi abin da ake bukata game da haka.

Advertisement

Har ila yau, Dakta Labaran ya bayyana cewa mai Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gina cibiyar kiwon lafiya a matakin farko guda daya a kowace mazaba a jihar Kano, ya kara da cewa suna nan suna tantance bukatun gaggawa na dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar don gabatar wa gwamna yankunan da ke da tsananin bukatar cibiyoyin lafiya.

Ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin dawo da yaki da cututtuka masu kashe yara kanana, inda ya koka da cewa bayan Covid-19, an yi watsi da allurar rigakafi ta yau da kullun ta yadda Kano ta zama jihar da tafi kowace jiha yawan yaran da ba a yi wa alluran rigakafi ba kwata-kwata a fadin wannan kasa.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa cutar mashaki (diphtheria) ta ta’azzara. Kano ce jihar da ta fi fama da cutar domin kashi 80 cikin 100 na masu fama da cutar a Najeriya suna jihar Kano.

Advertisement

“Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa mai girma Gwamna ya yi alkawarin sake dawo da alluran rigakafin da aka saba yi. Mun fara hakan, kuma na yi imanin za a ci gaba da yin hakan a duk tsawon lokacin gwamnatinmu,” in ji Kwamishinan.

Dakta Labaran cikin farin ciki ya bayyana cewa suna gab da cika alkawarin da mai girma gwamna ya dauka na gina babban asibiti a kowace karamar hukuma a jihar nan, inda ya jaddada cewa suna tantance kananan hukumomin da ba su da manyan asibitoci domin mika rahoton ga Gwamnan don daukar matakin da ya dace.

Advertisement

“Wani alƙawari mai muhimmanci game da kiwon lafiya da mai girma gwamna ke cikawa shi ne na kawata asibitocinmu. Mun fara da Asibitin Kwararru na Murtala Muhammadl, wanda shi ne babban asibitin al’umma mafi girma a Afirka ta Yamma, muna aikin gyaran sashin bayar da agajin gaggawa na asibitin. Idan mun gama,, za mu ci gaba da sauran sassansa daga nan kuma mu koma sauran asibitocin,” in ji shi.

Kwamishinan ya yaba da irin nasarorin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na ganin an tsaftace samu cibiyoyin koyar da ilimin kiwon lafiya na jihar kamar yadda ya yi alkawari.

Advertisement

Ya nuna matukar bacin ransa kan yadda ake samun yawaitar abubuwan da ba su dace ba da wadanda suka saba ka’ida a makarantun da gwamnati ta gano, yana mai cewa an dauki tsattsauran mataki kan daya daga cikin makarantun domin dawo da martabar makarantar da ta zube.

“Makarantun za su koma aiki kamar yadda aka saba. Daga wannan lokaci babu almundahana wajen shiga makaranta, babu rashin da’a, sannan babu daukar dalibai fiye da kima. Mun kuma gano cewa lokutan tantance darussan makarantun don tabbatar da ingancin su sun kare ko kuma suna gab da karewa. Mai girma Gwamna ya ba mu kudaden sabunta su tare da sauran aikace-aikacen waɗannan makarantun.

Advertisement

“Don haka, ina kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba wa gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf goyon baya, domin ya zo da kyakkyawan tsari, da manufodi, da jajircewa, da da kuma kudirin ciyar da jihar gaba ta kowane fanni na rayuwar al’ummar jihar”, Dr. Labaran ya kammala.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending