Connect with us

News

Iyayen Marayu A Jihar Kano Na Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Tabarbarewar tattalin arziki da ya biyo bayan cire tallafin man fetur a kasar nan, ya tilastawa mata da Iyayen marayu a Kano gudanar da zanga-zangar lumana, inda suke bukatar hukumomi su dauki matakin magance matsalolin tsadar rayuwa.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Kano ta ce ta Siyo kayan abinci da ya kai naira biliyan 1 da dubu dari 6 domin rabawa talakawa kyauta, sai dai ba a fayyace ranafara rabon tallafin ba da kuma yadda za a raba.

Kasar Kamaru Ta Gargadi Gwamnatin Najeriya Akan yiyuwar Samun Ambaliyar Ruwa A Wasu Jahohin Kasar nan

Matan da suka fito daga Ja’een da makwaftan unguwanni dake kananan hukumomin Gwale da Kumbotso, ana tsaka da ruwan sama da yammacin ranar lahadi sun sha alwashin yin tattaki har zuwa gwamnatin Kano domin isar da kokensu.

Advertisement

Sun yanke shawarar cewa tallafin ba dole ba ne ya kasance kyauta, maimakon hakan a rage farashin abincin domin mutane masu yawa su samu damar amfana.
Shugabar masu zanga-zangar, Habiba Sulaiman Umar da Maryam Abdullahi Muhammad, sun ce yanayin tattalin arzikin ya gurgunta kananan sana’o’insu na cikin gida.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending