News
Koda An Gyara Matatun Man Fetur Ɗin Najeriya, Mai Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 – IPMAN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya ta ce ba zai yiwu farashin man fetur ya yi kasa da Naira 200 ba, ko da an gyara matatun mai.
Kungiyar ta lura da hakan ne biyo bayan wani rahoto da aka buga kwanan nan, inda kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta ce farashin man fetur zai fadi kasa da Naira 200 kan kowace lita idan matatun sun sake fara aiki.
Yan Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Saboda Zabtare Kudaden Mutane Da Bankuna Ke Yi
Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya reshen jihar Ribas Joseph Obele, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar an gyara matatun man kasar kamar yadda aka tsara.
Ya ce, “Har sai matatun man kasarmu sun fara aiki, farashin mai zai ci gaba da karuwa saboda sauyin yanayi na kasa da kasa. Amma idan matatun mu suka yi aiki, ‘yan Najeriya za su sayi mai kasa da Naira 200 kan kowace lita.
“Rashin dala ya sa masu shigo da man fetur ke da wuya su ci gaba da shigo da su daga waje. Kimanin makonni biyu ke nan, sarkar rarraba man fetur ta fuskanci tashin hankali. Wannan ya bayyana a kan tashar saye da sayar da mai na NNPC.”
Da yake zantawa da jaridar The PUNCH, babban jami’in gudanarwar kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta Najeriya, Tunji Oyebanji, ya ce canjin dala na shafar farashin man fetur.
Ya kuma ce farashin danyen mai a kasuwannin duniya na kan hauhawa saboda yawan bukatu da rage da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta yi.
Wani labarin kuma Yan Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Saboda Zabtare Kudaden Mutane Da Bankuna Ke Yi
Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.
Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.
Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.
