Connect with us

News

Dan Sahu ya Maida Miliyoyin Ku’di daya Tsinta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wani matashi dake tuka Babur din Adaidaita Sahun a jihar Kano, mai suna Auwalu Salisu, ya dawo da wasu kudi Saifa Milyan 10 da dubu 130 sai kuma sama da Naira Milyan 2, wanda mallakin wani mai suna Alhaji Ibrahim Barka ne, daga ƙasar Chadi da aka manta a babur dinsa ranar Alhamis din data gabata.

Kwamishinan lafiya ya ce gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar gyara asibitocin jihar. 

Bayan ganin kuɗin a cikin Adaidaita Sahu dinsa, ya koma inda ya sauke fasinjan ko zai ganshi amma bai tarar dashi ba, sai ya kai kudaden wajen iyayensa, har suka sake komawa tare da mahaifinsa ko za’a samu mai kuɗin, amma basu samu ba, sai suka ajiye har suka samu sanarwar cigiya a guda cikin Gidajen Rediyon dake Kano, kuma suka dauki lambar da aka bayar, har suka mayar da kuɗin.

Wani labarin kuma Kwamishinan lafiya ya ce gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar gyara asibitocin jihar. 

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending