News
Kwamishinan lafiya ya ce gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar gyara asibitocin jihar.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar gyara asibitocin jihar.
Dakta Labaran ya yi wannan batu ne a lokacin da yake wani taro na farko da manyan daraktocin kula da lafiya na manyan asibitoci a dakin taro na hukumar kula da manyan asibitoci.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Kwamishinan ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa bangaren lafiya na jihar muhimmanci, ya kara da cewa gwamnan yana da tsarin da zai inganta tsarin kiwon lafiya na jihar Kano.
Dakta Labaran ya bukace su da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu domin gudanar da ayyuka masu inganci.
“Na yi ta zagayawa ina lura da kayan aiki musamman da dare, ina ganin duhu gaba daya, wurare kadan ne da mutum zai ga haske. Wannan ba abin yarda ba ne. Dole ne ku yi kananan ayyukan kula da asibitocinmu.” in ji Kwamishinan.
Cikin farin ciki ya sanar da taron cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta gyara asibitocin jihar, yana mai jaddada cewa duk wani asibitin da aka gyara dole ne shugabancin ya kula da sh yadda ya kamata.
Sai dai ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake rarraba ma’aikata a asibiti, inda ya ce mutum na iya zuwa asibiti da safe ya samu ma’aikata da dama a ofis ba sa yin komai, sannan ya dawo da yamma ko dare ya tarar da mutum daya ne ke kula da sashen baki daya, inda ya bukace su da su canja domin hakan bai dace ba a wajen ma’aikatar lafiya da kuma HMB.
Dakta Labaran ya ce, “Dole ne mu bi ka’ida. Dole ne yi abin da ya dace. Ban san wata doka da ta ce jami’in lafiya da safe kawai zai zo aiki ba. Abu daya da na lura da shi shi ne yawancin ma’aikatan suna ganin kansu kamar manajoji ne kawai, wadanda za su rinka zuwa aiki da safe kawai. Wannan ita ce matsalar da muke fama da ita.
“Wannan ba abu ne da za a amince da shi ba. Idan mutum yana ganin shi da safe kadsi zai rinka zuwa aiki, kawai ya yi murabus ya kafa wanda zai gudanar da kansa. Amma in dai mutum na son yin aiki, to dole ya yi aiki bisa ka’ida. Wannan ita ce hanya mafi sauki ta warware wannan matsalar. Idan da safe kawai za ka zo aiki, ga hanyar fita nan.
“A matsayinka na shugaba, dole ne ka zo aiki da wuri. Kar kuma ka bar rashin da’a a tsakanin ma’aikatanka kuma ka yarda da haka. Dole ka kasance a wurin aiki da wuri. A matsayinka na CMD, ya kamata ka kasance a asibiti kafin karfe 8 na safe don ka tabbatar dukkan sassa suna da mafi ƙarancin adadin ma’aikatan da ake bukata don aiki ya tafi yadda ake so. Yi misali a aikace domin su yi koyi.”
Daga nan sai Kwamishinan ya umarce su da su yi amfani da iliminsu da karfinsu wajen tafiyar da ma’aikatan da suke da su, ya kuma bukace su da su kasance masu taka tsantsan wajen amfani da kudaden da cibiyoyin ke samarwa, inda ya jaddada cewa kamata ya yi a yi amfani da kudaden wajen sauya fasalin asibitin da sayen kananan kayan aikin da ba su fi karfinsu ba.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na Hukumar kula da Manyan Asibitoci na jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayyana cewa Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zo da sauye-sauye masu ma’ana a harkar kiwon lafiya a jihar.
Dakta Nagoda ya yi nuni da cewa, sakamakon halin al’umma na kin yarda da sauyi, akan samu ma’aikata sun zauna a asibiti sama da shekaru 14 zuwa 15, inda ya koka da cewa canja karamin ma’aikacin lafiya daga wannan asibiti zuwa wani sai ya haifar da tayar da jijiyar wuya daga sassa daban-daban na jihar.
Ya bayyana cewa, domin jawo hankalin ma’aikata su himmatu wajen gudanar da ayyukansu, zai sanya kyautar Naira 100,000 duk wata uku ga duk karamin ma’aikacin da ya fi kwazo a matsayin tagomashi na jajircewar da ya yi, yana mai cewa dukkan shiyyoyi 14 na hukumar za su shiga wannan gasar.
Sakataren Zartarwar ya yi nuni da cewa, hakan zai zama kalubale ga sauran ma’aikata takwarorinsu ta yadda za su dage da wajen tabbatar da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, inda ya ce za a lika hoton wanda ya yi nasara a shalkwatar HMB a matsayin ma’aikaci mafi kwazo a wannan lokacin.
A ƙarshe, mahalarta taron sun ba da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin kiwon lafiya na jihar zuwa matakin da ake so don samun ingantaccen sakamako a kowane lokaci.