News
Wani Mutum Ya Rataye Kansa A Jahar Adamawa Saboda Matsin Rayuwa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani mutum ya kashe kan sa ta hanyar rataya a Unguwar Rumde-Baru, da ke karamar hukumar Yola ta Arewa a Jihar Adamawa.
Wata majiya mai tushe ta ce “mutumin zai kai shekara 29 zuwa 30, ya rataye kan sa ne sakamakon matsin halin rayuwar da yake ciki.
Hukumar NUC ta baiwa Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Jihar Katsina izinin fara kwasa-kwasai 14.
Haka kuma wani mazaunin Unguwar Ali Ibrahim, ya bayyana cewar “mutumin nan ya jima yana cewa wata rana zai kashe kansa saboda matsin halin rayuwa, muna ganin wasa yake sai ga shi yau ta tabbata.
“Idan ka gaza samar wa iyalinka abin da za su ci, idan ka gaza biya wa yaranka kudin makaranta, ka gaza biyan kudin wuta, me zai hana ka, ka nemi aikata abin da wannan mutum ya aikata?” ya tambaya.
“‘Yan Nijeriya na cikin wani mayuwacin hali, mutum ya wayi gari bai san me zai yi ya samu kwabo ba, ko ni da nake maka magana, ban san me iyalina za su ci nan gaba ba, muna rayuwa ne babu fata sam, idan da akwai fata haka ba zai faru ba.
“Ina fata gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu, za ta dauki matakin gaggawa kan matsanancin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki,” in ji Ali Ibrahim.
Ita ma dai rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin kakakinta, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tana gudanar da bincike bisa dalilan da ya kai ga mutuwar mutumin.
Nguroje, ya ce “jami’an ‘yansanda da kwararrun likitoci suna gudanar da bincike kan dalilan da suka kai ga aukuwar mutuwarsa,” in ji SP Yahya.
A wani labarin kuma Hukumar NUC ta baiwa Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Jihar Katsina izinin fara kwasa-kwasai 14.
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
