Connect with us

News

An kona zauren majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Barazanar Tsige Gwamna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

An kona zauren majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Barazanar Tsige Gwamna

Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin shirin tsige Gwamna Similanayi Fubara.

Daily Trust ta rawaito cewa maharin sun samu shiga majalisar dokokin ne a daren ranar Lahadi inda suka kona ta.

Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Yi Barazanar Kauracewa Ganawa Da Gwamnatin Tarayya a Gobe Litinin

Rahotanni na nuni da cewa daukin gaggawar da jami’an kashe gobara suka yi ne ya hana gobarar bazuwa a harabar majalisar baki daya.

Advertisement

Kokarin da aka yi na zantawa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ya ci tura a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

An tsaurara matakan tsaro a harabar ginin yayin da jami’an kashe gobara ke fafatawa don shawo kan gobarar.

A wani labarin kuma Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Yi Barazanar Kauracewa Ganawa Da Gwamnatin Tarayya a Gobe Litinin

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending