News
An Cire shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Tashin Gobara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar Ribas ya dauki wani salo a ranar Litinin yayin da majalisar ta cire Edison Ehie a matsayin shugaban masu rinjaye.
Daily Trust ta rawaito cewa Edison Ehie babban mai goyon bayan Gwamna Similanayi Fubara ne. An ce ya ba da kunya ga yunkurin fara yunkurin tsige gwamnan.
Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Zai Yi Zaman Gaggawa Akan Yakin Falasdinawa Da Isra’ila
Da yake sanar da tsige shugaban masu rinjaye a majalisar da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar, kakakin majalisar, Martins Amaehwule, ya ce an tsige shi ne saboda rashin halartar zaman majalisar.
Amaehwule yace kimanin yan majalisar 17 ne suka goyi bayan tsige dan majalisar.
A halin da ake ciki dai hukumomin tsaro sun mamaye harabar majalisar baki daya.
Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona zauren Majalisar.
Rahotanni na nuni da cewa hakan yafaru ne da nufin dakile shirin tsige gwamnan, wanda rahotanni suka ce ya samu sabani da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike.
