News
Wasu Mutum 2 Sun Mutu A Cikin Tankar Man Dizal A Jahr Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu mutum biyu, Philip Osando mai shekaru (40) da Philip Emmanuel mai shekaru (35) sun mutu a cikin wata tankar man dizel shatale-talen Baban Gwari, da ke kan titin zuwa Katsina.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana haka, ya ce hukumar ta samu wani kiran gaggawa da misalin karfe 08:20 daga wani sufeto Abubakar Surajo wanda ya kai rahoton faruwar lamarin kamar Leadership ta rawaito.
An Cire shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Tashin Gobara
Ya ce, “A lokacin da jami’anmu suka isa yankin da misalin 8:2, sun gano wasu mutane biyu, Philip Osando dan kimanin shekara 40 da kuma Philip Emernual dan kimanin shekaru 35 da haihuwa, wadanda suke harkokin kasuwancinsu kan titin Katsina.
“An ce wadanda abin ya shafa an musu alkawarin ba su kyautar man dizel amma kuma sai sun shiga cikin tankin dizal din don kwashe datti da dagelon da ke kasan tankin, shi ne suka shiga don cika sharadin da aka gindaya musu kafin su karbi man dizal din. Lokacin da direban babbar motar ya iso sai ya yi kokarin kiran daya daga cikinsu a waya sai bai ji an daga wayar ba.
“Can kuma da aka duba cikin takin sai aka same su a kwance cikin tankin dizal sun suma. Daga nan ne aka yi kokarin fito da su, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.
Abdullahi ya kara da cewa an mika gawarwakin mutanen biyu ga Sufeto Abubakar Surajo na ofishin ‘Yansanda na karamar Hukumar Dala, yayin da ake ci gaba da bincike don gano musabbabin rasuwarsu.
A wani labarin kuma An Cire shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Tashin Gobara
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News5 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News4 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News7 days ago
AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

