News
Ana Harbe-Harbe A Jahar Ribas Bayan Majalisar Jihar Ta Fara Shirin Tsige Gwama
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An harba bindigogi da barkonon tsohuwa a ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas da ke Fatakwal, bayan wasu ’yan majalisar sun fara kokarin tsige Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara.
Bayan barkewar harbe-harben dai, mutane sun rika guduwa domin tsira da rayukansu, yayin da jami’an tsaro suka rika kora mutane, ciki har da ma’aikatan da ofisoshinsu ke cikin harabar majalisar.
Bayanai sun nuna yanzu haka, ’yan majalisa 23, cikin har da shugaban majalisar, Martin Amaewhule, sun fara shirin tsige Gwamnan.
Kazalika, majalisar ta kuma tsige Shugaban Masu Rinjayenta, Edison Ehie, wanda ake zargin yana tare da Gwamnan.
Idan za a iya tunawa, ko a daren Lahadi sai da wasu da ake zargin hayar su aka dauka suka banka wa ginin majalisar wuta.
Jim kadan da aike wa Gwamnan takardar tsigewar dai, an ga ’yan majalisar wajen misalin karfe 8:15 suna ficewa cikin tsauraran matakan tsaro.
Lamarin dai ya dada tabbatar da zargin da ake yi na lalacewar alaka da Gwamna Fubara da tsohon maigidansa kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Bayan harbe-harbe da harba barkonon tsohuwa, mutane sun yi ta gudu yayin da ‘yan sanda suka fatattaki matafiya ciki har da ma’aikatan da ofisoshinsu ke a yankin.
A Wani labarin kuma Wasu Mutum 2 Sun Mutu A Cikin Tankar Man Dizal A Jahr Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
