Connect with us

News

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cin Zarafin Shugabanta, Joe Ajaero.

Published

on

DAGA KABIRUBASIRU

Gamayyar ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya na NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta shiga yajin aikin gama-gari sanadiyyar kamawa da kuma dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero.

Ƙungiyar ta sanar da batun yajin aikin, wanda zai gudana a ranar Laraba ne a wata tattaunawa da manema labaru ranar Juma’a, a Abuja.

zaben Gwamnan Kano :Alkalai suna hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran da INEC -Femi Falana

Shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun kuma bai wa Gwamnatin Tarayya sharuɗɗa shida da suke so a cika, ciki akwai sauke kwamishinan ƴan sanda na jihar Imo, da babban jami’in ƴan sanda na yankin da lamarin ya faru bisa zargin su da hannu a ‘cin zarafi da kuma wulaƙanta Mista Ajaero da sauran ƴaƴan ƙungiyar.”

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending