Connect with us

News

Kungiyar Tallafa wa Marayu da Marasa Karfi ta HOLPI da Gidauniyar BUA Sun Raba Tallafin Abinci

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

A ci gaba da kokarinta na tallafar rayuwar marayu da marasa karfi a cikin al’umma, Kungiyar Tallafa wa Marayu da Marasa Karfi ta HOLPI (Hope for Orphans and Less Privileged Initiative), ta hada gwiwa da Gidauniyar BUA don raba shinkafa ga marayu da sauran mabukata.

Rabon kayan tallafin, wanda aka yi bisa kulawar I Care Women and Youth Initiative, an gudanar da shi cikin nasara inda iyayen marayu da marasa karfi 60 suka amfana.

Yakin Israila Da Hamas Na Barazanar Haifar Da Yakin Duniya Na 3 -Kawu Sumaaila

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na  Kungiyar Tallafa wa Marayu da Marasa Karfi ta HOLPI Ibrahim Abdullahi ya tura da Jaridar Inda Ranka

 

Advertisement

Da take jawabi a madadin shugabar HOLPI Hajiya Bilkisu Muhammad Rabi’u, Nusaiba Rabi’u Danshareef, ta bayyana cewa burin HOLPI a kullum shi ne samar da farin ciki da walwala ga marayu da marasa karfi, musamman a wannan lokaci da rayuwa ta yi wa jama’a tsanani.

 

Ta ce hakan ne ya sa HOLPI kullum take kai kawo wajen samo hanyoyin da za a rinka tallafa wa mabukata da kayan abinci da na masarufi daga daidaikun mutane da kungiyoyi masu tallafa wa al’umma.

 

Nusaiba ta ci gaba da cewa, gamsuwa da ayyukan HOLPI ya sanya Gidauniyar BUA ta ba ta buhun shinkafa 60 don raba wa marayu da marasa karfi da ke samun taimakon HOLPI, tana mai yaba wa Gidauniyar bisa bayar da tallafin tare da alwashin za a raba su ga wadanda suka cancanta.

 

Advertisement

Wakiliyar shugabar ta tabbatar da cewa HOLPI za ta ci gaba da kokari kamar yadda ta saba, tana mai jan hankalin iyayen marayu da su kara kula da tarbiyyar marayun da ke hannunsu kasancewar Allah zai yi musu tambaya kan wannan amana da Ya ba su.

Da take jawabi, Hajiya Fiddausi ta I Care Women and Youth Initiative, masu sa ido kan yadda ake raba tallafin da Gidauniyar BUA ke bayarwa, ta ce shugaban kamfanin BUA ya himmatu wajen tallafa wa al’umma a lungu da sako na jihar Kano duba da halin kunci da ake ciki tun daga lokacin barkewar annobar korona.

Ta ce, Gidauniyar kan tallafa wa mutane da kayan abinci da na masarufi don a rage musu radadin matsin rayuwa da ake fama da shi a wannan kasa, tana mai yaba tsarin da HOLPI ke da shi na raba kayan tallafi ga marayu da marasa karfi tare da jaddada kudirin Gidauniyar BUA na ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar Kano kamar yadda take yi.

Zilai Nasidi da Zara’u Musa, wasu da suka amfana da tallafin, sun gode wa HOLPI da Gidauniyar BUA bisa yadda suke tallafar rayuwar jama’a da kayan abinci da sauran abubuwan bukatar tafiyar da rayuwa.

Sun yi addu’ar ci gaba da samun taimakon Allah ga kungiyoyin biyu bisa tallafar rayuwar al’umma da suke yi, tare da tabbatar da cewa za su yi amfani da abin da aka ba su wajen ciyar da marayun da ke hannunsu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending