News
Gwamnatin Tarraya Ta Fusata Kungiyar ASUU
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar malaman jami’o’i ASUU da kwamitin shugabannin jami’o’in Najeriya sun yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na cire kashi 40 daga kudaden shiga na jami’o’i.
Gwamnatin tarayya, a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 17 ga Oktoba, 2023 mai dauke da sa hannun Akanta-Janar ta Tarayya, Mrs Oluwatoyin Madein, ta ce za ta fara cire kudin daga watan Nuwamba na 2023 kamar yadda daftarin kudi na ranar 20 ga watan Disambar 2021 ya nuna.
Kungiyar Tallafa wa Marayu da Marasa Karfi ta HOLPI da Gidauniyar BUA Sun Raba Tallafin Abinci
Da yake mayar da martani, Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka ya fusata kungiyar saboda jami’o’in ba sa samun kudaden shiga daga wasu kuɗaɗe da ake dawainiyya ga dalibai.
A nasa bangaren, babban sakataren kwamitin shugabannin jami’o’in Najeriya Farfesa Yakubu Ochefu ya ce kudaden da ake cirewa a baya sun kai kashi 25 amma yanzu ya karu zuwa kashi 40.
Arewa radio ta rawaito cewa Ya yi kira ga Akanta Janar da ta fayyace abin da ake nufi da yunkurin, yana mai cewa jami’o’in suna karbar kudin dawainiya ne kawai daga dalibai ba riba ko kudaden shiga ba.
A wani labarin kuma Kungiyar Tallafa wa Marayu da Marasa Karfi ta HOLPI da Gidauniyar BUA Sun Raba Tallafin Abinci
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
