Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Ware N2Bn Domin Gudanar Da Wasu Manyan Aikin Tituna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware kudi naira biliyan biyu a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 domin gudanae da wasu manyan aikin titunan jihar.

Gwamna Malam Umar Namadi shine ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar.

Advertisement

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Dr Nasir Yusuf Gawuna Shine Zababben Gwamnan Jahar Kano

Ya ce an sake gabatar da wasu kudi Naira biliyan biyu a cikin kasafin kudin domin aikin inganta titin Hadejia zuwa Garun Gabas da kuma sanya masa kwalta.

 

Advertisement

Malam Umar Namadi ya kuma ce an ware naira biliyan biyu da milyan dari biyar domin aikin titin Kwanar Girimbo zuwa Gantsa da kuma Sara.

 

Advertisement

Ya ce an kuma bada kudi naira biliyan biyar domin gina titunan cikin gari, wadanda suka hada da kammala aikin Wurno da Kanya Babba da fara gudanar da aikin Gumel Bye Pass da Kafin Hausa da Dansure da Gandun Sarki da Bulangu da Aujara da Basirka, da Dangyatum da kuma Sankara. Hakazalika gwamann yace an ware kudi naira biliyan dari bakwai a kasafin kudin domin gina gada da manyan kwalbatoci a

fadin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending