Connect with us

News

Gwamnatin jihar Kano Zata Ci Gaba Da Aikin Titina Masu 5Kilomiter A Kanan Hukumomin Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da sake bude cibiyoyin koyon sana’oin dogaro da kai guda 26 da gwamnatin data gabata ta rufe su.

Kwamishinan aiyuka da gidaje na jihar Kano, Alhaji Marwan Ahmad, Ya baiyana cewar an samar da cibiyoyin ne a zamanin tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ganin mata da matasa sun koyi sana’oi daban daban.

Advertisement

DSS Ta Gayyaci Tsohon Minista, Hadi Sirika

Ya kara da cewar cibiyoyin zasu taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar shaye-shaye da sata a jihar nan.

Ya kuma baiyana cewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci ‘yan kwangilar da suke aikin shimfida titi mai tsawon kilomita biyar a daukacin kananan hukumomin jihar Kano, da su dawo bakin aikinsu batare da bata lokaci ba.

Advertisement

Hakazalika ya ce an dawo ci gaba da aikin ruwan Jakara dake cikin birnin kano wanda shima tsohuwar gwamnati ta yi fatali da shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending