Connect with us

Sports

Za a yi gwanjon rigunan Lionel Messi na Kofin Duniya

Published

on

Lionel Messi

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Za a yi gwanjon rigunan wasa shida daga cikin rigunan da Lionel Messi ya saka a lokacin wasannin Argentina a gasar Kofin Duniya ta 2022 da aka yi a Qatar

Kyaftin Messi, mai shekara 36, ya ɗaga kofin ne bayan da suka doke Faransa a a wasan karshe na gasar.

Advertisement

Innah Lil Lahi Wa Innah Ilaihir Rajiun: Allah yayiwa Darakta a masana’antar shirya fina finai ta Kannywood

Rigarsa ta wasan ƙarshe na kunshe cikin jerin rigunan da ake sa ran za su samu sama da fam miliyan takwas a gwanjon da Sotheby ta shirya a birnin New York.

Rigar ƙwallon ƙafa wanda ta fi daraja ita ce ta Diego Maradona da ya sanya a gasar Kofin Duniya ta 1986, wacce aka sayar kan fam miliyan 7.1 a shekarar 2022.

Advertisement

Brahm Wachter, shugaban masu tara kayayyaki na zamani na Sotheby, ya ce sayar da riguna shida na Messi “ya zama babban abin alfahari a tarihin gwanjon kaya”.

Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, ya zama ɗan wasa na farko a tarihin gasar Kofin Duniya da ya ci kwallo a kowanne mataki a gasar, tun daga rukuni har zuwa wasan ƙarshe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending