News
An fasa gidan yari tare da sakin fursunoni a Kasar Saliyo
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotonni daga Saliyo na cewa an kai hari gidan yari tare da sakin fursunoni, jim-kaɗan bayan jin ƙarar harbe-harbe a Freetown babban birnin ƙasar da safiyar yau Lahadi.
Wani jami’in da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin ‘Pademba Road’ da ke tsakiyar birnin Freetown tare da sakin fursunoni.
Kowa Na Da Irin Gudummuwa Da Zai Bayar Dan Hana Mace Macen Mata Masu Ciki — Dakta Habib Sadauki
Kawo yanzu ba a sa adadin fursunonin da suka tsare ba.
Da safiyar yau ne mazauna birnin suka ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu da ke birnin.
Harin gidan yarin na zuwa ne bayan da hukumomin ƙasar, suka yi kira ga ‘yan ƙasar da su kwantar da hankula, suna masu cewa sun shawo kan matsalar.
Cikin sanarwar da shugaban ƙasar, Julius Maada Bio ya fitar daga fadarsa, ya ce an maido da zaman lafiya, tare da ƙaddamar da farautar maharan.
Ƙungiyar Ecowas da Amurka sun yi Allah wadai da lamarin
Tuni dai aka sanya dokar hana fita a faɗin ƙasar
A wani labarin kuma Kowa Na Da Irin Gudummuwa Da Zai Bayar Dan Hana Mace Macen Mata Masu Ciki — Dakta Habib Sadauki
Masu ɗinkin tufafin mata sun gudanar da zanga-zanga a Afghanistan musamman a birnin Herat bayan hukumomin Taliban sun tilasta masu rufe shagunansu.
Daya daga cikin maɗinkan ya ce rayuwa ta yi tsanani a Afghanistan saboda ƙaruwar talauci da rashin ayyukan yi.
Babu dai wata sanarwa daga shugabannin Taliban game da matakin.
Hukumomin Taliban ɗin dai sun ɗauki matakin rufe makarantun mata da kuma hana matan zuwa jami’a tun bayan da suka ƙwaci mulki shekaru biyu da suka gabata
