Connect with us

News

Mutane 13 sun jikkata a wani hatsarin  mota a  babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Akalla fasinjoji 13 ne suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin da ya afku a hanyar Legas zuwa Ibadan.

Hatsarin motan ya afku ne da sanyin safiyar  yau Lahadin  a kusa da Car Park C, a jihar Ogun.

Advertisement

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta tabbatar da afkuwar hatsarin ga jaridar DAILY POST, inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:55 na safe.

Kakakin hukumar FRSC a jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce jami’an hukumar sun gaggauta kai dauki domin gudanar da aikin ceto.

Advertisement

A cewarta, jimillar mutane 22 ne hatsarin ya rutsa da su, maza 21 manya da mace daya.

“Mutane 13 sun jikkata (manyan 12 da babba mace daya). Babu wani rai da ya yi hasarar hatsarin,” in ji Okpe.

Advertisement

Ta kara da cewa hatsarin ya rutsa da wasu manyan motoci guda uku masu lamba: KBT205XB, KJA230Y da DUT35XE.

Haka kuma ta hada da wata mota kirar Toyota Corolla mai rijista a matsayin MUS793HM da wata motar bas Toyota Hiace mai lamba FG369-F20.

Advertisement

Abubuwan da ake zargin sun haddasa hatsarin ne, sun hada da toshe hanyoyin mota da gudu, lamarin da ta ce ya kai ga rasa yadda za a shawo kan lamarin.

“An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Farobis Mowe Lotto don kula da lafiyarsu,” in ji ta. A halin da ake ciki, Kwamandan sashin Ogun na FRSC, Anthony Uga, ya shawarci masu ababen hawa da su rika yin taka tsantsan a lokacin da suke kan hanya,.

Advertisement

A wani labarin kuma Kotu ta bada dama Ajaka da SDP su binciki kayayyakin zaɓen Kogi

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending