News
Sojoji Sun Kwato Mutane 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Kebbi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dakarun Bataliya ta daya Barikin Dukku da na ‘yan banga a jihar kebbi sun yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama a dajin karamar hukumar Shanga da ke Jihar Kebbi.
Nasarar da aka samu ta biyo bayan wani aikin ceto da rundunar hadin gwiwa da jami’an tsaro suka yi a dajin karamar hukumar Shanga bayan rahoton wadanda aka yi garkuwa da su.
A cewar daraktan tsaro, AbdulRahman Usman, maza shidan da aka ceto duk sun kasance cikin koshin lafiya da kuma walwala da jin dadi kuma an mayar da su cikin iyalansu.
Ya bayyana cewa dakarun Bataliya ta 1 na Dukku Barrack da ke Birinin Kebbi tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin sun kai wani samame a tsaunin Kogon Damisa da ke kusa da Saminaka a karamar hukumar Shanga, wani gari mai iyaka tsakanin Kebbi da Jihar Neja.
A cewarsa, a yayin samamen, rundunar ta fatattaki ‘yan bindiga da dama tare da ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su.
An sanar da jami’an tsaro a yankin da suka hada da sojoji da ‘yan banga inda suka shiga cikin dajin Shanga, an yi nasarar ceto wadanda harin ya rutsa da su.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
