Connect with us

News

Dakaru sojojin sun kashe ƴan ta’adda 180 sun kama 204 cikin mako guda

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojojin a cikin makon jiya sun kashe ƴan ta’adda 180, sun kama wasu 204 sannan sun ceto mutum 234 da aka yi garkuwa da su.

Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fidda ranar Juma’a.

Kungiyar SERAP Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15

Premium Times ta ruwaito cewa Buba ya ce dakarun sun kama makamai da suka hada da bindigogi 46, harsasai 148, motoci 34, wayoyin hannu da dama, babura 47 da kudi naira miliyan 1.5 da dai sauran kaya daga hannun maharan.

A Arewa maso Gabas Buba ya ce dakarun dake ƙarkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan ta’adda 19, sun kama 52 sun ceto mutum 134 a aka yi garkuwa da su a cikin makon.

Advertisement

Ya ce dakarun sun kama manyan bindigogi AK-47 6, harsasai 58, motoci uku, wayoyin hannu 8, babura uku, Keke daya, da rigar kare harsashi harsashi biyu.

Buba ya ce dakarun sun Kama wasu da ake zargi ‘yan Boko Haram/ ISWAP a karamar hukumar Chibok sannan sun gudanar da sintiri a kananan hukumomin Kukawa, Bama da Gwoza a jihar Borno.

Ya ce dakarun sun kama masu garkuwa da mutane da masu hakar ma’adinai a karamar hukumar Fulani dake jihar Yobe.

Buba ya ce dakarun sun kama bama-bamai kirar IEDs a kananan hukumomin Monguno, Mafa da Gwoza a jihar Borno.

Dakarun sun kashe JAS/ISWAP a Madagali dake kananan hukumomin Adamawa da Maiduguri dake jihar Borno.

Buba ya ce ‘yan ta’adda 91 da suka hada da maza 13, mata 35 da yara 43 sun mika wuya.

Advertisement

Ya ce rundunar sojin sama dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a ranar 24 da 25 ga Nuwamba sun yi wa mahara ruwan bama-bamai a Tagoshe da Chongolo Kura a Borno inda suka kashe mahara 130 a harin.

A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven da Whirl Stroke’sun kashe mahara da dama a jihohin Niger, Benuwe, Filato da Taraba.

Ya ce rundunar sojin sama a ranar 26 ga Nuwamba sun Kai hari maɓuyar shahararren dan bindiga Ali Kawaje dake Dagam a karamar hukumar Shiroro jihar Niger inda a nan suka kashe mahara da dama.

Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun kama 37 sannan sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su.

Ya ce rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ sun kashe mahara biyar, sun kama 10 kuma sun ceto mutum daya da aka yi garkuwa da shi.

A Arewa maso Yamma Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ da ‘Whirl Punch’ sun kashe mahara da dama a jihohin Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara.

Advertisement

Ya ce dakarun sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a mabuyar mahara dake karamar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara ranar 25 ga Nuwamba.

“Rundunar Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan ta’adda 14, sun kama 20 sun ceto mutum 88 da aka yi garkuwa da su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending