News
Gwamnatin Tarraya Ta Biya NairaMilliyan 52 Domin Sakin Fursunoni 399 A Jihar Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A kokarin da take yi na rage cinkoso a gidajen gyaran hali, gwamnatin tarayya ta biya tara da kuma diyya na Nairamilliyan 52 ga fursunoni 399 a cibiyoyi daban-daban a fadin jihar Kaduna.
Kwanturolan hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Kaduna, Dr Ado Saleh ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da shirin a Zaria a ranar Litinin, inda ya ce an sako fursunonin 68 daga cibiyoyi na gyaran hali na Zaria da Makarfi da Soba da kuma Ikara.
Ya ce tun da farko an saki fursunoni 110 a Kaduna, inda ya ce bikin da aka yi a Zaria ci gaba ne na shirin da gwamnatin tarayya ta tsara tare da aiwatarwa.
Kwanturolan ya kara da cewa za’a baiwa kowane daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin Naira dubu 10 a matsayin kudin Mota domin komawa gida.
A wani labarin kuma Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano tare da hadin gwiwar BAN sun shirya taron wayar da kan ‘yan jaridu a kan cutar mashako
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
