Connect with us

News

Akwai Bukatar Hafsoshin Tsaron Najeriya Su Ajiye Mukamansu – Farfesa Usaman Yusuf

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma mamba a kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Usman Yusuf ya yi kira ga manyan jami’an sojojin Najeriya su yi murabus daga kan mukamansu sakamakon harin da jirgin yaki ya kai kan fararen hula a Kaduna ranar Lahadi.

Yusuf ya ce a wani yanayi na daban, akwai bukatar dukkan hafsoshim soji su mika takardar murabus dinsu kan hadarin da ya jefa kasarnan cikin alhini.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Ya kuma bayyana cewa rundunar Sojoji ba za su iya bincikar kanta ba, don haka ya kamata a samu wani kwamiti mai cikakken iko, mai zaman kansa karkashin wani babban Alkalin Alkalan Najeriya mai ritaya, domin ya binciki al’amarin.

Ya ce kasashen waje za su yi shakkar sayar da makamai ga sojojin Najeriya muddin suna Afkawa Fararen hula.

Advertisement

A wani labarin kuma ‘Yan sanda sun kama mutane 15, sun kwato motoci 20 da aka sace a Kano

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending