Connect with us

News

‘Yan sanda sun kama mutane 15, sun kwato motoci 20 da aka sace a Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Talata ta sanar da kama wasu mutane 15 da ake zargi tare da kwato motoci 20 da aka sace a sassa daban-daban na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Ya ce an  kama tare da kwato motocin da aka sace ya samo asali ne sakamakon jajircewar da rundunar ta yi na kawo karshen duk wasu laifuka a jihar.

Kiyawa ya ce, “Mun himmatu sosai wajen yakar satar motoci da duk wani nau’in aika aika a wuraren da muke sa ido.

Advertisement

“A cikin wata daya da ya gabata, rundunar ‘yan sandan ta ci gaba da nuna aniyar ta na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin daukacin mazauna jihar.

“Rundunar ‘yan sandan jihar ta dauki matakin ne ta hanyar yaki da sace-sacen jama’a a kan matsalar satar motoci a jihar.

Daily News24 ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sanda, Usaini Gumel, yayin da yake yaba wa jama’a bisa fahimtarsu, hadin kai da goyon bayansu,

Ya kuma bukaci kowa da kowa ya ci gaba da kai rahoton duk wani motsi ko mutum ko wani abu da ya same shi a ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin daukar matakin tsaro cikin gaggawa.

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending