Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

A ranar Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 28, wanda ya gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Baya ga halartar taron, shugaban ya gana da Sarki Charles na Ingila, da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, da shugabannin kasashe da dama.

Kotu Ta Daure Matashi Wata 6 Kan Satar Magi Da Sabulu

Har ila yau, shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kara kaimi tsakanin Nijeriya da Jamus domin inganta wutar lantarki a Nijeriya, ya kuma shirya wani babban taro tare da masu ruwa da tsaki da masu zuba jari kan kasuwanci a Nijeriya da shirin kaddamar da motocin bas amfani da wutar lantarki.

A ranar 29 ga watan Nuwamba, 2023, Tinubu ya bar Abuja zuwa Dubai domin halartar taron da ake sa ran kammalawa a ranar 12 ga watan Disamba, 2023.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Gwamnatin Tinubu ta sha suka kan wakilai 1,411 da Nijeriya ta tafi da su domin halartar taron, amma gwamnatin ta ce mutane 422 ne kawai ta tura domin halartar taron.

A wani labarin kuma Kotu Ta Daure Matashi Wata 6 Kan Satar Magi Da Sabulu

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta jaddada cewa babu wani wuri Falasɗinawa za su iya zuwa don ɓuya daga hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza.

“Mun faɗa mun sake faɗa,” in ji hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa ta UNRWA cikin wani saƙo a dandalin X. “Muna sake faɗa, babu wani gidan ɓuya a Gaza.”

Ta ƙara da cewa: “Wahalar da ɗana’dam ke sha kai ba zai ɗauka ba. Cigaba da kai hare-hare da kuma faɗaɗa su zuwa kudancin Gaza na ƙara maimaita bala’in da aka fuskanta a ‘yan makonnin da suka wuce.”

UNRWA na wannan magana ne yayin da rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta na kai samame a tsakiyar biranen Gaza uku, ciki har da Khan Younis – birni mafi grima a kudancin Gaza.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending