Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Raba Tallafi Ga Masu Kananan Masana’antu

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Nan bada dadewa ba gwamnatin tarayya za ta fara raba tallafi na musamman ga masu kananan masana’antu wannan na daga cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na rage musu radadin matsin da janye tallafin man fetur ya jawo.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Ministar masana’atu da kasuwanci, Dakta Doris Uzoka-Anite, ta kuma kara da cewa, shirin ya kunshi tsarin tallafi kashi biyu, za kuma a raba wa kananan masana’antun da suka cika dukkan ka’idojin da aka gindaya.

Advertisement

Sanusi Lamido Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Sauka Daga Mukaminsa Ministan Man Fetur 

Sanarwar ta kuma kara da cewa, a cikin kashi na farko za a raba wa kananan masana’antu N50,000 a kananan hukumomi 774 da ke fadin tarayyar kasa nan.

“Gwamnatin tarayya za ta hada hannu da ma’aikatan masana’antu da kasuwanci da hukumnar kula da kananan masana’antu za kuma a nemi hadin kan gwamnati jihohi da kananan hukumomi da kuma ‘yan majalisun tarayya da bankuna da kuma dukkan masu ruwa da tsaki don ganin an samu nasarar rarraba kudaden.

Advertisement

“Kananann masana’antun da suka cancanta za su samar da takardun shaidan da suka kamata wadanda suka hada da shaidar irin sana’ar da suke gudanarwa da shaidar dan kasa da na karamar hukumna da kuma takardun shaidar bude ausuun banki.”

Leadership ta ruwaito cewa Kananan masana’antun da suka amfana da bashin naira miliyan 1 za su biya ne a cikin shekara 3 yayin da wadanda suka amfana da naira biliyan 1 za su biya a cikin shekara 5.

Advertisement

A wani labarin kuma Sanusi Lamido Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Sauka Daga Mukaminsa Ministan Man Fetur 

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending