News
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya Nada Sabuwar Shugabar Kwalejin Aikin Jinya Da Ungozoma
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A ci gaba da jajircewa wajen sake sauya fasalin Kwalejin Koyon Aukin Jinya da Ungozoma domin yin aiki mai kyau da inganci, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Bara’atu Gwadabe a matsayin sabuwar shugabar kwalejin.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fito daga sashin hulda da jama’a na ma’aikatar aka raba wa manema labarai, ciki har da Jaridar Inda Ranka.
Gwamatin Jihar Kano Za Ta Sake Bude Sabon Asibitin Masu Tabin Hankali.
Kwamishinan ya bayyana cewa nadin na nan take ne, kuma ya biyo bayan gogewa da sadaukarwa da Bara’atu Gwadabe take da su a matakai daban-daban na aikin aikin gwamnati, musamman a bangaren lafiya.
Dakta Labaran ya umarce ta da ta yi aiki tukuru domin tabbatar da amincewar da aka yi mata tare da bayar da gudummawarta a kokarin da ake yi na kawo sauyi a cibiyoyin ilimi na kiwon lafiya da ma daukacin bangaren lafiya na jihar baki daya, wanda mai girma Gwamna ya fara.
Bara’atu Gwadabe, wadda aka haifa a shekarar 1967 a unguwar Galadanchi da ke jihar Kano, ta yi karatun firamare da na gaba da firamare duk a jihar Kano, a tsakanin 1976 zuwa 1985.
A 1987, ta samu shiga Makarantar Koyon Aikin Ungozoma. Bayan kammalawa, ta shiga Makarantar Samun Horo a Aikin Jinya a 2004 da ta kammala a 2006.
Sabuwar Shugabar ta samu aiki da Hukumar Kula da Manyan Asibitoci Jihar Kano a matsayin jami’ar aikin jinya a shekarar 1990 kuma ta yi aiki a wurare daban-daban da suka hada da Cibiyoyin Lafiya ta Fuskar Yamma, Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Asibitin Yara na Hasiya Bayero, Asibitin Haihuwa na Sabo Bakinzuwo, Asibitin Haihuwa na Nuhu Bamalli, da dai sauransu.
Sha’awarta ga koyarwa ya sanya a shekarar 2010 ta tafi Kwaalejin Fasaha ta (Kaduna Polytechnic) inda ta karanci ilimin aikin jinya da ta kammala a shekarar 2014. Ba ta samu kammalawa a kan lokaci ba sakamakon yawan yajin aikin da aka rinka yi. Kammalawarta ke da wuya, sai ta wuce zuwa Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha (Maryam Abacha American University) da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar, inda ta samu digiri a fannin aikin jinya (B.sc Nursing).
Bayan ta dawo ne sai aka tura ta sashin kula da ilimin aikin asibiti na Makarantar Horar da Aikin Jinya Domin ta kula da lamuran dalibai.
Kafin nadin nata, Bara’atu Gwadabe ita ce Darakta a Babbar Makarantar Horar da Aikin Jinya da Ungozoma (School of Post Basic Midwifery) da ke karamar hukumar Gezawa, mukamin da take rike da shi tun 2018.
