Connect with us

News

Hukumar FRSC  Na Shirin Farautar Manyan Motoci Masu Dakon Dabbobi Hade Da Mutane

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane 18 a wani hadarin mota da ya afku a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar Lahadi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Bisi Kazeem ya sanya wa hannu, ta ce hatsarin ya afku ne da karfe 05:20 na Asuba a kauyen Audu Jhangon da tireloli dauke da mutane da dabbobi wadanda da alama matafiyan dare ne.

Yadda Gwamna Katsina Dikko Raɗɗa ya fafata gumurzu da ‘yan bindiga a dajin Safana

Ya ce hatsarin ya rutsa da mutane 65 daga cikinsu, mutane 27 da suka samu raunuka daban-daban an kai su asibiti mafi kusa domin yi musu magani.

Ya kara da cewa, biyo bayan afkuwar al’amarin, shugaban hukumar, Dauda Biu, ya kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta gudanar da aikin sintiri na musamman domin kamo tireloli da manyan motoci dauke da mutane hade da dabbobi.

Advertisement

A wani labarin kuma Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum a  hanyar jihar Kaduna zuwa Abuja

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending