Connect with us

Politics

Jamiyyar PDP ta yi martanin bayan sauyin shekar ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers zuwa APC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP ta nemi hukumar zaben kasar INEC ta gudanar da sabon zabe don cike gibin da ta ce an samu bayan sauyin sheka da wasu ‘yan majalisar dokoki a jihar Ribas suka yi.

Jam’iyyar ta dage a kan cewa lallai sai ‘yan majalisar dokokin jihar 27 sun sauka daga kujerunsu.

Advertisement

Victor Osimhen ne gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023

Da safiyar ranr litinin ne aka ba da rahotannin cewa ‘yan majalisar dokokin jihar sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP wadda a doronta ne aka zabe su, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ana kallon matakin a matsayin wani sabon babi da rikici siyasa tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike da gwamnan jihar mai ci, Siminalayi Fubara.

Advertisement

Kwanan baya ne rahotanni suka ce, ana yunkurin tsige gwamnan daga kan kujerarsa.

 

Advertisement

Nyesom Wike dan jam’iyyar PDP, wanda amma ya karbi mukami a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta APC, ya shiga takun-saka da jam’iyyar tasa tun kafin babban zaben kasar, lokacin da ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa.

 

Advertisement

Wasu masu sharhi na cewa sauyin shekar da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas suka yi a ranar Litinin din nan, mai yiwuwa sharar fage ce ga yunkurin komawar minista Wike zuwa jam’iyya mai mulki, amma dai ba ta taba ji ya ambata ba a bainar jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending