Sports
Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta koma saman teburin firimiya bayan doke Brighton
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar kwallon kafar Arsenal tayi nasarar komawa saman teburin gasar Firimiya sakamakon nasarar da ta samu a kan Brighton da ci 2-0.
Gabriel Jesus da Kai Haverts suka jefawa Arsenal kwallayenta guda 2 a mintina 53 da 87, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ba tare da an jefa kwallo ba.
Gwamnatin Jahar Kano Ta Fara Bincike Akan Gobarar Da Ta Tashi A Sakatariyar Gwale
Wannan nasarar ta baiwa Arsenal damar samun karin maki 3, abinda ya kawo adadin makinta zuwa 39 daga wasanni 17 da tayi.
Yanzu haka kungiyar na matsayi na farko da maki 39, sai Aston Villa a matsayi na 2 da maki 38, sannan Liverpool a matsayi na 3 da maki 37, yayin da ita Liverpool take karawa da Manchester United yanzu haka.
Sauran sakamakon wasannin da aka yi yau lahadi sun nuna cewar, Aston Villa ta doke Brentford da ci 2-1, sai kuma West Ham da ta doke Wolves da ci 3-0.
Ita kuwa West Ham ta na matsayi na 7 ne da maki 27.
Manchester City da ta tashi 3-3 da kungiyar Crystal Palace a ranar asabar na matsayi na 4 da maki 34.
-
News24 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
