Connect with us

News

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 437.3.

Published

on

Advertisements
ads

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 437.3.

Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar a zaman majalisar da ya gabata a yau Laraba.

Bayan sace sarki da fadawa 22 a Taraba, ‘yan bindiga sun sungumi Mai Shari’a

 Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ta ruwaito cewa gabatar da shirin ya share fagen karatu na uku da zartar da kasafin kudin.

Shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar, da ya gabatar da kwafin kasafin kudin shekarar 2024 domin mikawa Gwamna Abba Yusuf gaba domin amincewar sa.

Advertisement

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala) ya shaida wa NAN jim kadan bayan kammala zaman majalisar cewa kasafin zai samar da ayyukan raya kasa amfanin jihar.

“A cikin kasafin kudin, an ware kashi 67 bisa 100 na manyan ayyuka, yayin da kashi 33 na kudaden s aiyukan Yau da kullum

Ya ce ilimi ya samu kaso 30 cikin dari sai kuma kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

Prime time News ta ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf a ranar 27 ga watan Oktoba ya gabatar da kasafin kudin mai taken: “Budget of Change and Consolidation”, ga majalisar domin amincewa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending