News
Ba a Samu Fasa Gidan Yari Ba a Shekarar 2023 – NCoS
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD MUHAMMAD
Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya, NCoS, ta ce ba ta samu fasa gidajen yari da kai hare-hare ba a dukkan cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya 253 da ke fadin kasar a shekarar 2023.
Mai magana da yawun, Mataimakin Kwanturola na hukumar (ACC) Abubakar Umar ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
Umar ya ce gwamnati ta dauki kwararan matakai na karfafa matakan tsaro da kuma dakile duk wata barazana da za ta iya tasowa daga ciki ko wajen gidajen yarin da ake dasu.
A cewarsa, Najeriya ta sha fama da munanan abubuwan da suka faru na tashe tashen hankula da kai hare-hare a shekarun baya, inda ya kara da cewa an samar da dabaru da dama don hana faruwar al’amura a fadin kasar.
Ya tunatar da cewa hukumar ta sanar a ranar 20 ga watan Janairu cewa shekarar 2023 za ta kasance shekara mai wahala ga masu aikata laifuka a fadin kasar nan, yayin da aka tura dimbin ma’aikata da fasahar tattara bayanan sirri don dakile duk wasu kai hare-hare gidajen yari.
Wannan, ya ce duka biyun sun shafi cigaban ababen more rayuwa a hidimar 2023 da dabarun tsaro don hana abin da ya faru a shekarar 2022.
Idan zaku Iya tuna cewa wani lamari ya faru a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2022, wanda ya shafi kungiyar ISWAP, inda suka yi nasarar kai wani hari a cibiyar gidan yari da ke Abuja.
