News
Yadda Ta Kasance A Kotun Koli Akan Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yau Alhamis 21, ga watan Disambar 2023, Kotun kolin Nijeriya da ke Abuja ta fara sauraren karar zaben gwamnan Kano da Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf da Jam’iyyar NNPP da INEC suka shigar gabanta.
Ma su shigar da karar sunan kalubalantar hukuncin kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano da Kotun daukaka kara da su suka ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
A zaman na yau, tunda farko Kotun ta ce, ba ta da lokacin sauraren ƙarar NNPP da Abba da INEC da suka shigar gabanta har guda tara (9), sai dai su zaɓi guda ɗaya a cikin tara.
Daga bisani Kotu ta yi ƙarin haske kan batun satar ƙuri’un zaɓe a Nijeriya, wanda ta ce wajibi ne doka ta yi aiki don magance matsalar ba a iya Kano kaɗai ba a duk faɗin Nijeriya saboda wajibi ne kiyaye doka da oda.
A karshe Kotun ta kammala sauraron ƙarar, ta kuma ce za ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari’ar.
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News18 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
