Connect with us

News

Yanzu-Yanzu: An Saki Emefiele daga gidan Yari bayan ya cika sharadan Beli

Published

on

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya cika sharuddan belin da mai shari’a Hamza Mu’auz na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja dake Maitama ya bayar.

Mai shari’a Mu’auz ya bayar da belin Mista Emefiele a kan kudi Naira miliyan 300.

Advertisement

Yanzu-Yanzu: An Saki Emefiele daga gidan Yari bayan ya cika sharadan Beli

An kuma bukaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda tabbas sai sun kasance sun mallaki wata kadara a gundumar Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Solace Base ta rahoto.

An tattaro cewa sammacin sakin Mista Emefiele yana dauke da sa hannun alkalin hutu, mai shari’a Othman Musa a ranar 22 ga watan Disamba.

Advertisement

Wata majiya a gidan yarin da ta bayyana sakin tsohon gwamnan na CBN ta ce, “An saki Emefiele cikin nutsuwa a gidan yarin Kuje da karfe 3 na yammacin ranar Juma’a bayan ya cika sharuddan belinsa a asirce.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na ci gaba da nemansa domin ta kama shi,” kuma shi ya sa aka sake shi a asirce.

Advertisement

Ya ce an yi komai a asirce tare da hadin gwiwa da jami’an gidan yarin da suka kammala shirin tare da boye shi daga maziyartan da suka ziyarci gidan yarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending