Connect with us

News

EFCC Ta binciken wasu Kamfani 52 Kan Mu’amalar Ta’addanci a karkashin jagorancin tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta na binciken wasu kamfanoni 52 kan hada-hadar kudaden waje da babban bankin Najeriya CBN.

Hukumar ta EFCC na binciken kudaden da aka ware wa kamfanoni 52 karkashin jagorancin tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.

Rundunar Ƴan sanda sun kama likitan da ya yi wa wata budurwa allurar zubar da ciki ta mutu a Kano

Hukumar ta rubuta wa kamfanoni daban-daban suna neman takardu kan hada-hadar cinikinsu a cikin shekaru 10 da suka gabata, kamar yanda Jaridar TheCable ta ruwaito. 

Wasu daga cikin kamfanonin da ake binciken sun hada da Dangote Group, BUA Group da kuma Flour Mills – amma duk sun musanta aikata ba daidai ba a sadarwar su da EFCC.

Advertisement

A baya SaharaReporters ta rawaito cewa jami’an hukumar EFCC sun gudanar da bincike a babban ofishin kamfanin Dangote a Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an na EFCC sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a lokacin Emefiele a matsayin Gwamnan CBN.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rahotanni na nuni da cewa kamfanin Dangote ya ce a shirye yake yayu bayanin duk wani abu da ya shafi kasuwancin ta na forex domin ba ta karya wata doka ba.

Cikakkun bayanai na binciken hukumar EFCC har yanzu ba su da kyau amma da alama bincike ne akan manyan kamfanonin da suka samu kudaden shiga daga CBN a karkashin Emefiele.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending