Connect with us

News

Ɗaurin shekaru 14 ne hukuncin masu digirin bogi dan kwatano -Bulama Bukarti

Published

on

Barista Bulama Bukarti

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Ɗaurin shekaru 14 ne hukuncin masu digirin bogi dan kwatano -Bulama Bukart

Advertisement

Masana Shari’a a faɗin ƙasa Najeriya sun fara sambaɗo nasu sharhi game da badaƙalar takardun digirin Bogi da wasu ƴan ƙasa Najeriya ke mallaka daga jami’o’in ƙasar Benin.

Ina ba a manta ba a farkon makon nan ne gidan Jaridar Daily Nigerian ta Wallafa wani binciken ƙwaƙwaf da ta yi game da masu siyo karatun digiri a Kwatano.In da suka Wallafa daki daki yadda suka aika ma’aikacin su ya yi ɓadda kama ya samo musu sahihan bayanai game da ita wannan digiri da ake ganin rashin ingancin ta.

Advertisement

Tinubu ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar cika shekaru 61 a duniya.

Wannan bincike dai ya tada ƙura a kafofin daban daban inda masana kan harkokin shari’a irin su Barista Bulama Bukarti suka fito suka bayyana nasu sharhi game da lamarin,A wata hira da BBC ta yi da shi ya

Advertisement

 

Ya ce tabbas akwai waɗanda suka yi ingantacciyar digiri a ƙasashen Benin da kuma Togo haka kuma akwai waɗanda suka mallaki ta Bogi amma sai dai Barista ya ƙara da cewa kafin a iya ware waɗanda suka yi sahihin karatu dole sai an yi bincike ingantacce wanda shi ne za iya tantance sahihi da kuma bogi. Kuma ya bayyana cewa mallakar takardar karatu na Bogi hakan babban laifi ne ga wanda ya aikata.

Advertisement

 

”In aka duba sashi na 362 na kundin tsarin har zuwa sashi na 380 za a ga cewa sun yi bayanai dalla-dalla game da aikata wannan laifi,inda suka tanadi cewar idan mutum ya mallaki ko ya ƙirƙiri takardar ƙarya za a iya masa hukuncin da zai kai ɗaurin shekara sha huɗu a kurkuku,Haka kuma Babban laifi ne ka gabatar da kanka ga hukumar Yiwa ƙasa hidima (NYSC) kace musu ka gama jami’a ka cancanci hidimar ƙasa bayan kai da kanka ka san Bogi ce,Shima hakan laifine da mutun zai iya zama gidan kaso na shekara biyu.”

Advertisement

A wani labarin kuma Tinubu ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar cika shekaru 61 a duniya.

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending